Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Corona ta sa an rage kasafin kudin Cricket a Australia

Published

on

Hukumar shirya wasan Cricket a kasar Australia (CA) , ta rage Dala miliyan 40 na kasafin kudin gudanar da wasannin sakamakon Annobar cutar Corona.

Hukumar tace, ta rage Dalar kasar ta Australia har miliyan 40, tare da dakatar da wasu ma’aikata da kuma dage gasar Australian tour, don rage kashe wasu kudaden sakamakon tsaiko da Annobar ta kawo a harkoki da dama na wasanni a Australia.

Shugaban hukumar (CA) Earl Eddings, ya ce mawuyacin halin da aka shiga ne ya haddasa hakan.

Eddings, ya sanar da cewar ba shi da tabbas kuma abu ne mawuyaci a gudanar da gasar cin kofin duniya mai taken T20, da aka shirya zai gudana a kasar ta Australia a bana , sakamakon cutar ta Corona mai lakabin Covid-19.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!