Labaran Kano
An dakatar da yin kilisa a Kano
Masaraurtar Kano ta sanar da soke yin atisayen dawakai ga daukacin al’ummar masarautar.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da masarautar ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun Turakin Kano Alhaji Lamido Abdullahi Sanusi wanda shi ne shugaban kwamitin Durbar na masarautar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa an dakatar da hawan angwanci har sai an fito da tsare-tsare masu kyau da nagarta da za a sanar da jama’a a nan gaba.
Haka kuma sanarwar tace daga yanzu an dakatar da kilisar motsa dawakai, da aka saba yi bisa al’ada, matukar ta haura dawaki 3 zuwa 5, sannan tilas su kasance cikin kyaky-kyawar shiga ta kamala, sannan ba a yarda ayi sukuwa a inda bai kamata ba, kamar lunguna, da kan tituna, da kuma duk inda zai kawo barazana ga lafiyar jama’a.
Masarautar ta Kano ta ce, ta dauki wannan mataki ne biyo bayan yawaitar korafe-korafe da ake samu game da hawan Dawakai barkatai, marasa dalili da sukwane-sukwanen ‘yan atisaye da ke jawo buge kananan yara da mata, musamman wadanda suka manyanta da kuma ta’addancin bata-gari dake jawo asarar dukiyar al’umma.
You must be logged in to post a comment Login