Labarai
An fara babban taron koli na ECOWAS a Abuja

Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS sun hallara a birnin Abuja don bude babban taron koli da za’a fara yau Lahadi.
Bayanai sun ce rashin tsaro da kuma juyin Mulki musamman masu sarkakiya da aka samu a Guinea Bissau da kuma yunkurinsa a jamhuriyar Benin za’a fi mayar da hankali a yayin wannnan ganawa ta musamman.
Taron na zuwa ne mako guda kacal bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a Benin kan shugaban kasar Patrice Talon a kwatano, tare da rikicin siyasa a Guinea-Bissau da kuma tabarbarewar tsaro a arewacin kasashen gabar tekun yammacin Afirka.
Wannan shi ne taron koli na farko da Shugaban kasar Sierra Leone Julius Maada Bio ke jagoranta a matsayin shugaban ECOWAS, inda ake sa ran zai jagoranci yanke muhimman shawarwari kan tsaron yankin.
You must be logged in to post a comment Login