Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

ECOWAS zata gudanar da taron gaggawa kan juyin mulki a Nijar

Published

on

Shugabanin kungiyar kasashe mambobin ECOWAS, zasu gudanar da wani taron gaggawa ranar Lahadi game da juyin mulkin kasar Nijar a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata  sanarwa da shugaban kungiyar ta ECOWAS kuma shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya fitar,inda ya sha alwashin kawo karshen matsalar juyin Mulki a yammacin Africa.

Ta cikin Sanarwar, Shugaba Tinubu ya yi fatan wannan taron na su zai samar da matsaya guda wadda zata bada damar mayar da jamhuriyar Nijar kan turbar Dimokradiyya.

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris da sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Gutteros sun bukaci Bola Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen dawo da martabar jamhuriyar Nijar ta hanyar kwato ta daga hannun Sojoji a wata tattaunawa da su ta wayar tarho.

Rahoton: Ummulkhairi Rabi’u Yusuf

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!