ilimi
An fara jin ra’ayoyin malamai kan samar da hukumar hana bara a Kano – Baba Impossible
Gwamnatin Kano ta fara gayyato rukunin malamai a Kano domin tattaunawa tare da jin ra’ayin su kan samar da hukumar da za ta hana barace-barace a kan titi.
Kwamishinan ma’aikatar kula da addinai Muhammad Tahar Baba Impossible ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ganawar sa da malaman.
“Gwamnatin ta gayyaci malaman ne don fahimtar da su abinda hukumar za ta mayar da hankali akai idan aka samar da ita” in ji Baba Impossible.
Baba impossible ya kuma ce “Daga cikin waɗanda gwamnatin taji ra’ayoyin su akan samar da hukumar sun haɗa da masu kare haƙƙin ɗan Adam”.
Da dama daga cikin malaman da suka halarci tattaunawar sun nuna goyon bayan su kan samar da hukumar.
A makon da ya gabata ne gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, za a samar da hukumar da za ta hana barace-baracen almajirai akan titinan jihar.
You must be logged in to post a comment Login