Kasuwanci
An fara kera Fensir a Najeriya
Wani kamfani a nan gida Najeriya ya fara kera fensira ta hanyar amfani da tsaffin jaridu .
Ministan kimiyya da fasaha Dr. Ogbonnaya Onu ne ya bayyawa cewar kamfanin zai fara samar da akalla pensira fiye da miliyan biyu a duk shekara wanda ya fi karfin amfani birane da yankuna kadai.
Da yake Magana jiya a Abuja yayin da ya karbi bakuncin gangun wani kamfanin da ke samar da pensira na Bamib ya ce’ mun yaba da yadda kake gudanar da ayyukanka na cigaban kasa.
Ya ce a wata ziyara da suka kai wani kamfanin samar da fensira a jiha Enugu , ‘mun tarar da su suna gudanar da bincike akan fensira, abin takaici ne sakamakon kasar nan bata da wani kamfani da ke samar da fensira a Najeriya .
A da akwai wasu kamfanunuwa da suke sarrafa fensira amma dukkaninsu sun dakushe a yanzu, hakan ce ta sa a matsayina na ministan kimiyya da fasaha na ga dacewar sarrafa shi a Najeriya duba da yadda daliban mu na firamare da ma wasu yan sakandare da ke amfani da fensir.
Minister Onu ya ce a ganinsa fensir ba wani a zo a gani ba, ya kuma zama wajibi a ce Najeriya tana samar da fensiran da take amfani da su.
Ya ce mun basu shekara biyu domin samar da adadin fensiran da ake bukata, yana mai cewa samar da fensiran ya dauki hankali na, domin kuwa duk kayayyakin da ake kera fensiran muna da shi a Najeriya, hakan dai zai samar da ayyukan yi ga matasa
Ministan ya ce kawo yanzu an samu cigaba domin zasu tabbatar da cewar an samar da dukkanin kayayyakin a nan gida Najeriya, tare da cewar tuni gwamnatin Akwa Ibom suka fara kira fensira wanda wannan wani cigaba ne.