Labarai
INEC ta ƙaddamar da kwamitin kula da jigilar kayayyakin zaɓen 2027

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta ƙaddamar da kwamitin kula da jigilar kayayyakin zaɓe, domin ƙarfafa shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya ƙaddamar da kwamitin a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da isar da kayayyakin zaɓe zuwa rumfunan zaɓe a kan lokaci.
Ya ce kwamitin zai yi aiki tare da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, domin magance matsalolin sufuri da za su iya kawo tsaiko wajen gudanar da zaɓen.
An naɗa Rear Admiral Jamila Abubakar-Sadiq mai ritaya a matsayin shugabar kwamitin, wadda za ta jagoranci tsara hanyoyin jigilar kayayyakin zaɓe cikin tsari da inganci.
You must be logged in to post a comment Login