Labarai
Majalisar Dattawa ta bukaci a kamo Mele Kyari a raye ko a mace

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin asusun gwamnati ya bayar da umarnin kamo tsohon Babban Daraktan Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, bayan ya kasa halartar zaman bincike kan zargin wasu kuɗaɗe da suka kai Naira tiriliyan 210 da ake zargin ba a yi bayaninsu yadda ya kamata ba tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023.
Shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo mai wakiltar Gombe ta Arewa, ya ce duk inda Mele Kyari yake, a kamo shi a kawo shi gaban kwamitin. Kafin yanke wannan hukunci, Sanatoci Abdul Ningi, Victor Umeh, Peter Nwaebonyi da tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, sun bayyana cewa ci gaba da jinkirta binciken zai rage martabar Majalisar Dattawa. Sai dai Sanatoci Saliu Mustapha da Tony Nwoye sun roƙi a ba Kyari ƙarin lokaci saboda rahoton cewa yana jinya a Jamus.
A nasa bangaren, tsohon Babban Jami’in Kuɗi na NNPCL, Umar Isa, ya musanta zargin bacewar kuɗin, yana mai cewa jimillar kuɗaɗen da kamfanin ya samu a lokacin da ake binciken sun kai kusan Naira tiriliyan 54.5 ne kawai. Ya ce zargin bacewar Naira tiriliyan 210 ba shi da tushe, tare da kira ga hukumomin EFCC da NFIU su gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya.
You must be logged in to post a comment Login