Ƙetare
An gano gawarwaki 270 bayan zaftarewar ƙasa Darfuf

Wani jagoran farar hula a wani yanki na Darfur na kasar Sudan da ke ƙarƙashin ikon ‘yan tawaye ya ce an gano gawarwaki 270, bayan zaftarewar ƙasa da ta afka wa wani ƙauye da ke kan dutse.
Shugaban hukumar yankin, Mogeeb al-Rahman, ya ce ana kyautata zaton ɗaruruwan mutane maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan duwatsun.
Wani Bidiyo ya nuna yadda mazauna yankin ke haƙar ƙasa da hannayensu domin ceton rayuka.
A ranar Talatar da ta gabata ne, ƙungiyar ‘yan tawayen ta ce kusan duk mazauna ƙauyen waɗanda yawansu ya kai 1,000 sun mutu, in banda mutum guda kacal da ya tsira.
Sai dai rahotonni sun bayyana cewa, hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da suka rasu ba kawo yanzu.
You must be logged in to post a comment Login