Connect with us

Labarai

An hallaka mutane 6 a sabbin hare-haren Filato

Published

on

Mutane shida ne suka rasu a  jihar Filato ciki har da mace guda a hare-hare daban-daban da suka auku a yankunan Bassa da Mangu. 

 

Har ila yau, mutane goma sha biyu sun jikkata wadanda su ke kwance a asibiti suna samun kulawa.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin farko ya auku ne a kauyen Ancha da ke karamar hukumar Bassa, sai kuma wani hari na biyu a Gyenbwas Rinji da ke karamar hukumar Mangu.

 

Kafin haka kuma, wasu mutane hudu sun mutu, biyu kuma sun jikkata a wani hari a Uwok-Ishe, yayin da suke hanyarsu zuwa wuraren hakar ma’adinai.

 

Shugaban kungiyar Gan Allah Fulani (GAFDAN), Garba Abdullahi, ya ce mutanen da aka kashe a harin farko sun bace ne da misalin karfe 3 na dare yayin kiwon shanu. Daga bisani, aka tsinci gawawwakin su a kauyen Ancha.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!