Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An kaddamar da dakarun duba masu corona gida-gida

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta kaddamar da jami’an da za su rika zuwa har gida suna duba masu fama da cutar corona a kananan hukumomi 8 na kwaryar birnin Kano karkashin wani shiri na musamman da masu cutar zasu rika samun kulawa har gida.

 

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da jami’an.

 

Ya ce, ma’aikatar Lafiya ta lura da yadda ake samun jinkiri a yayin da aka kira jami’an da za su duba masu cutar corona, wanda haka ne ya sanya ta samar da jamia’n don samun agajin gaggawa.

 

Dakta Tsanyawa ya kara da cewar Ma’aikatan zasu rika duba wadanda aka killace a gidansu amma da zarar jikin ya rikice za’a kai mutum zuwa cibiyar killacewa don samun kulawa sosai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!