Labarai
An kama wadanda ake zargin kashe matukiya ta farko na jiragen yaki
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar cafke wadanda ake zargi da kashe mace ta farko matukiyar jirgin saman sojin kasar nan Tolulope Arotile a watan da ya gabata.
Mutanen biyu da ake zargi sun hada da Nehemiah Adejo da David Adejo an gurfanar da su a gaban kotun magistire da ke jihar ta Kaduna.
Hakan na cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ta Kaduna Muhammad Jalige ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa a jiya Laraba an gurfanar da wadanda ake zargi a kutun majistire inda ake tuhumar su da laifuka hudu da yayi sanadiyyar mutuwar Arotile, da suka hadar da tukin ganganci da rashin nutuswa da kuma tuki ba tare da lasisi ba har ma da laifin yin tuki ba tare da bin doka ba wanda hakan ke barazana ga rayuka da dukiyiyin al’ummar da basu jib a basu gani ba.
Sai dai wadanda ake tuhuma da laifin sun bukaci kotu da ta bayar da belin su akanm naira miliyan daya kowannen su.
Sanarwar ta kara da cewa, yayin da mai shari’a Emmanual Benjamin y adage zaman saurar shari’ar zuwa ranar 24 da 25 ga watan da muke ciki na agusta.
You must be logged in to post a comment Login