Labarai
An kama wani matashi da kwalaben kodin 149- NDLEA
Hukumar Hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani Mai suna Bashir Umar, dan shekaru Talatin da Biyar, Mazaunin Unguwar Hotoro Ladanai da kwalaben kodin Dari da Arbain da Tara da ake zargin yana safara da dilanci a yankin hotoro da sauran Unguwanni a nan Kano.
Shugaban hukumar ta NDLEA a nan Kano Abubakar Idris Ahmad ne ya bayana hakan, yayin zantawarsa da freedom rediyo a ranar Laraba.
Kwamandan hukumar wanda maimagana da yawun hukumar Sadiq Muhammad Mai Gatari yayi Magana a madadinsa, ya ce wannan Bashi ne karo na Farko da suka kama magidancin ba.
Mai Gatari, ya ce zasu fadada bincike akan matashin tare da daukar matakin da ya dace.
Ko da kuma zanta da matashin da ake zargi, yayi mana karin bayani kan yadda ya shiga hanun hukumar.
Hukumar Hana sha da safarar miyagun kwayoyin ta kuma gargadi masu safara ko dilancin miyagun kwayoyi da su tuba kafin fadawa komar hukumar, tare da yin Kira ga masu kishin kasa wajen sanar da Hukumar bayanan Sirri, Dan dakile sha da safarar miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano da kasa baki daya.
You must be logged in to post a comment Login