Kiwon Lafiya
An kame wasu mutane 145 da zargin hadassa rikicin manoma da makiyaya
Wata majiya daga fadar Gwamnati ta tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta kasa ta kama mutane 145 da ake zargin suna da hannu a rikicin manoma da makiyya a sassan kasar nan da suka hada jihohin Benue da Kaduna da Nasarawa.
An dai kama mutanen ne a tsakanin watan Janerun shekara ta 2016 kawo watan janerun wannan shekarar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya baiwa hukumomin tsaro umarnin da su kama dukkanin wadanda ake zargi na da hannu cikin rikicin.
Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunan ta, ta bayyana cewar daga cikin wadanda ake zargin an gurfanar da mutum 124 a gaban kotu, a yayin da ake cigaba da gudanar da binciken mutum 21 kuma suke jiran a gurfanar da su gaban kotu.