Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FC Galadima na Zawarcin Dan wasan Diamond Star Aliyu Haidar

Published

on

Akwai yiwuwar kungiyar kwallon kafa ta Galadima dake karamar hukumar Gezawa a jihar Kano ta dauki dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Diamond Star mai suna Aliyu Haidar.

Mai horas da ‘yan wasan kungiyar ta Galadima, Lawan Tata ne ya sanar da hakan a wata zantawa da ya yi da gidan radiyo freedom a daren jiya Asabar 04 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Sojin ruwa sun buga wasan Golf a Kano

Tata ya ce kungiyar a shirye take da ta biya ko nawa aka saka a matsayin kudin dan wasan mai shekaru 15.

Tunda fari dai mataimakin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Galadima, Abbati Robinho ne ya nuna bukatar sayo dan wasan inda kuma shugaban kungiyar, Saifullahi Dawaki ya ce a shirye yake ya kashe ko nawane domin ganin sun mallaki dan wasan.

Kungiyar ta Galadima dai tana daga cikin manyan kungiyoyi da suke haskawa kuma suke taka rawar gani a garin na Gezawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!