Labarai
An kammala zaben tantance gwani kan shugabancin jami’ar Bayero
Jami’ar Bayero ta gudanar da zaben tantance gwani na ‘yan takara dake neman jagorancin shugabantar Jami’ar wato Vice Chancellor a tsawon shekaru biyar a gaba, bayan kammala wa’adin shugaban ta na yanzu Farfesa Muhammad Yahuza Bello.
Zaben wanda, ya gudana a harabar sabuwar jami’ar a yau Laraba, ‘yan Takara hudu ne da suka hada da Farfesa Dalhatu Balarabe Yahaya da Farfesa Adamu Idris Tanko sai Farfesa Sagir Adamu Abbas tare da Farfesa Muhammad Dikko Aliyu suka tsaya neman kuri’ar amincewar mukarraban jami’ar don fidda gwani a cikin su.
Mutum 1,512 masu matakin digiri na farko zuwa sama ne suka kada kuri’ar tantance gwani, wanda Farfesa Sagir Adamu Abbas ya samu galaba da kuri’u 1,026 sai Farfesa Adamu Tanko da 416, da Farfesa Muhammad Dikko Aliyu da ya samu kuri’a 10, ya yinda Farfesa Dalhatu Balarabe Yahaya ya samu kuri’a 05.
You must be logged in to post a comment Login