Connect with us

Labarai

An nada laftanal janar Tukur Yusuf Buratai a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar jamhuriyar Benin

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa tsohon babban hafsan sojan ƙasa na ƙasar nan, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar jamhuriyar Benin.

Haka zalika shugaba Buhari ya kuma amince da tura janar Abayomi Olonisakin, tsohon babban hafsan tsaron ƙasa a matsayin jakadan na Najeriya a ƙasar Kamaru.

A yayin wani biki da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya mikawa waɗanda aka naɗa takardar fara aiki.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen ƙasar nan ta fitar.

Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin haske kan inda aka tura tsohon babban hafsan sojin ruwa na ƙasar nan Vice Admiral Ibok-Ette Ibas da tsohon babban hafsan sojin sama Air Vice Marshal Sadique Abubakar da kuma Air Vice Marshal Muhammad Usman, tsohon babban jami’in leken asiri na shalkwatar tsaro ta ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!