Labarai
An rufe tashoshin sadarwa a kananan hukumomi 13 a jihar Katsina-Tsaro
A kalla kananan hukumomi 13 ne a jihar katsina aka rufe amfani da tashoshin sadarwa.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Hukumar Sadarwa ta Kasa NCC ta karyata shirin rufe tashoshin sadarwa a jihar ta Katsina.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hadar da karamar hukumar Sabuwa da Faskari da Dandume da Batsari sai Danmusa, da Kankara, da Jibia, da Safana, da kuma Dutsin-Ma.
Jaridar daily trust ta rawito sauran kananan hukumomin sun hada da Kurfi da Funtua, da Bakori da Malumfashi.
A baya-bayan nan dai Hukumar NCC ta karyata wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa hukumar ta umarci kamfanonin sadarwa da su rufe shafukan su a Katsina.
An rufe hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 13 a jihar Katsina-Tsaro
You must be logged in to post a comment Login