Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da mutane sun san amfanin Gero a jiki da sun rikeshi a matsayin abinci-Dakta Hakeem

Published

on

Masana ilimin tsirrai sun ce sinadaran Gina jiki da Gero ke dashi sun fi na sauran kayan abinci.

Masanan sun ce watsin da al’ummar yanzu su ka yi da Gero ne, yasa ake yawan samun bakin cutuka dake damun jikin dan Adam.

Shugaban cibiyar binciken Noma a kasashe masu zafi da ake Kira da Icrisat  Dakta Hakeem Ajeigbe, ne ya bayyana hakan yayin taron bikin noman Gero da cibiyar ta gudanar a garin wasai dake Karamar hukumar Minjibir.

Dakta Hakeem, ya ce Gero yana da sinadarin gina jiki fiye da gabakidayan kayan abincin da al’ummar ke sarrafawa.

A cewar shi da al’umma za su rungumi amfani da Gero a matsayin abinci da ba za su rinka kamuwa da cutukan da ake samu a yanzu ba.

Da yake jawabi Hakimin karamar hukumar Minjibir Alhaji Sama’ila Abdullahi S Fulani, ya bukaci manoma da su rinka amfani da irin shuka Mai inganci da noman zamani don Samar da abinci Mai inganci ga al’umma.

Wasu daga cikin manoman da suka halarci taron sun bayyana irin alfanun da suke samu a noma.

Yayin taron an sarrafa abinci kala-kala ta hanyar amfani da gero da suka yi dai-dai a kalar abincin da al’umma ke sarrafawa a yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!