Labarai
An sahale wa jiragen Nijeriya tashi daga Masar don dauko daliban Sudan
- Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta fara jigilar dakko dalibai dama sauran ‘yan kasar da suka makale sakamakon yakin da ya barke a Sudan.
- Ci gaban na zuwa ne ta cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen da ma’aikatar jin kai da kiyaye afkuwar bala’o’I suka fitar.
- A cewar gwamnatin tarayya hukumomin Najeriyar da ke Masar na ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Masar don kwaso daliban.
Gwamnatin Najeriya ta ce jirgin Air Force C-130H, da na Air Peace da karin wasu kamfanonin jigila sun samu sahalewar tashi daga, Masar domin dauko ‘yan kasar da suka makale sakamakon yakin da ya barke a Sudan.
Wannan ci gaban dai na zuwa ne ta cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar nan hadin gwiwa da ma’aikatar jin kai da kiyaye afkuwar bala’o’I ta kasa suka fitar a daren jiya alhamis, kan halin da ake ciki game shirin kwaso su zuwa gida Najeriya.
Haka zalika gwamnatin tarayyar ta ce hukumomin Najeriyar dake Masar na cigaba da tattaunawa da mahukuntan Masar din, kan shirin kwaso su, da samar musu da izinin gaggawa na shiga kasar, da kuma wajen zama zuwa lokacin da zasu taso zuwa gida Najeriya.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login