Labaran Wasanni
An sallami Pele daga Asibiti

Tsohon dan wasan kasar Brazil Pele ya koma gida bayan da aka sallameshi daga asibiti sakamakon jinya da ya sha.
Mai shekaru 80 ya kasance a bangaren masu kulawa ta musamman wato ICU tun a ranar 4 ga watan Satumbar daya gabata.
Mahukuntan asibitin ne dai suka sanar da sallamar Pele a wani rubutu da suka wallafa a shafin Internet a ranar Juma’a 01 ga watan Oktobar 2021.
Pele dan kasar Brazil wanda ya lashe gasar cin kofin Duniya har sau uku a shekarun 1958, 1962 da kuma 1970.
Kuma ya zama dan wasan guda da yafi kowa zura kwallo a tarihin kasar da yawan kwallaye 77 a wasanni 92 da ya buga.
You must be logged in to post a comment Login