Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Luis Suarez ya ci tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona

Published

on

Zakarun gasar La Ligar kasar Spain ta shekarar 2020/2021 Athletico Madrid sunyi nasarar doke Barcelona da ci 2-0 a wasan da aka gudanar yau Asabar 02 ga watan Oktoban 2021.

Karawar data gudana a filin wasa na Metropolitano dake birnin Madrid na kasar.

Dan wasa Thomas Lemar ne ya fara zura kwallon farko a mintuna na 22 da fara wasan, kafin daga bisani tsohon dan wasan na Barcelona Lius Suarez ya zura ta biyu a mintuna na 43 dab da zuwa hutun rabin lokaci.

Nasarar da Athletico Madrid ta yi ya bata damar komawa mataki na 2 a gasar da maki 17 cikin wasanni 8 data buga.

Yayinda Barcelona karkashin jagorancin Ronald Koeman ke cigaba da fuskantar Kalubalen rashin samun nasara a kungiyar.

  1. Wanda hakan ya sa Barcelona take a mataki 9 da da maki 12 wasanni 7 data buga.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!