Coronavirus
An samu karin mutum 11 na masu cutar Covid-19 a Kano
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce mutum 11 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Covid-19 a fadin jihar, ranar Alhamis,
Ma’aikatar ta wallafa hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce daga cikin mutum 1,176 mutane 11 aka samu na masu dauke da cutar.
Sanarwar ta ce mutum guda kacal aka samu ya warke daga cutar a ranar Alhamis.
daga cikin mutum 16,621 da aka yiwa gwajin cutar, mutum 1,302 ne aka tabbatar sun kamu da ita a Kano.
Yanzu haka mutum 220 ake da su na masu dauke da kwayar cutar a Kano.
An sallami mutum 1,030, yayin da ta yi ajalin mutum 50.
#COVID19KN Update as at 11:18pm 9th July 2020.
*️⃣ 11 new cases recorded from 1,176 results received today from the laboratories and 1 #COVID19Kano patient discharged.#MaskUpKano #FlattenedTheCurve #StaySafe @GovUmarGanduje @DGawuna@dr_tyw @TijjaniHussai11 @imagesharfadi93 pic.twitter.com/2UkbXZOQoK
— Kano State Ministry of Health (@KNSMOH) July 9, 2020
You must be logged in to post a comment Login