Labaran Freedom
An samu karuwar masu ta’amali da kwayoyi a Kano- NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA shiyyar Kano, ta ce, yawaitar kwacen wayoyin hannu da bata gari ke yi a hannun mutane da ake fuskanta a yanzu, na da alaka da karuwar masu shaye-shaye ciki har da mata.
Shugaban hukumar Abubakar Sadik Ahmad, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakiliyar Freedom Radio Halima Wada Sinkin.
Har ma ya ce, shaye-shaye da kwacen waya suna da alaka ta kusa domin idan bata garin suka rasa abinda za su sayi kayan maye su sha shi ke tilasta su yin kwacen wayar domin su siyar su samu kudi.
Latsa alamar Play domin sauraro.
You must be logged in to post a comment Login