Labarai
Majalisar Wakilai ta bukaci shugabannin tsaro su yi murabus

Majalisar Wakilai ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro da su yi murabus cikin mutunci idan har matsalar rashin tsaro ta ci gaba a kasar nan cikin wa’adin da za a ayyana a fili.
Majalisar ta kuma yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito da ingantaccen tsarin tsaro domin murkushe ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a fadin Najeriya.
Bukatar ta biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa mai wakiltar Arochukwu/Ohafia ta jihar Abia, Ibe Osonwa, ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan karuwar hare-hare musamman kan makarantu da kuma yadda sace dalibai ke kawo cikas ga harkar ilimi.
Haka zalika, majalisar ta gayyaci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, tare da shugabannin rundunonin tsaro domin yi wa ‘yan majalisa bayani kan matakan da ake dauka wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar.
You must be logged in to post a comment Login