Labarai
An shiga halin rudani a Kano biyo bayan rasuwar Yan majalisun dokoki 2

Al’ummar Jihar kano sun shiga rudani biyo bayan rasuwar Yan majalisun dokokin Jihar guda biyu da yammacin jiya laraba.
Tuni dai a gudanar da jana’izar guda Daga cikin su, Wato Dan majalisa Mai wakiltar karamar hukumar Ungogo Aminu Sa’adu Ungogo.
Kamar yadda Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Jihar Honorable Lawan Husaini Dala ne ya bayyana Hakan a zantawar su da wakilinmu Salisu Baffayo ta wayar tarho.
A yau alhamis ne Ake sa ran gudanar da jana’izar marigayi sarki Aliyu Daneji dan majalisa Mai wakiltar karamar birni kano.
You must be logged in to post a comment Login