Connect with us

Labarai

An tabbatar da mutuwar yaro dan shekara uku bayan shafe kwanaki cikin rijiya

Published

on

Wani yaro mai shekaru uku Abdura’uf Badamasi ya rasu bayan faɗawa rijiya a garin Wangara da ke Karamar Hukumar Tofa ta Jihar Kano.

Ta cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar kashe gobara ta Kano, Malam Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar aikewa Freedom Radio.

Sanarwar ta ce an samu kiran gaggawa inda aka sanar da ɓatan yaron tun ranar Alhamis, inda ake zargin ya faɗa cikin rijiya.

Ya ƙara da cewa jami’an ceto sun isa wurin tare da tsamo yaron daga rijiyar cikin mawuyacin hali, kafin daga bisani a tabbatar da rasuwarsa.

Hukumar Kashe Gobaran ta yi ta’aziyya ga iyayen yaron, tare da jan hankalin al’umma su rufe rijiyoyi da kuma kula da yara domin kauce wa irin wannan haɗari a nan gaba.


 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!