Labarai
An tsinci gawar wata mata da ta fara zagwayewa a Kano
A safiyar yau alhamis ne mazauna yankin ƴankusa sabuwar jidda a karamar hukumar Kumbotso da ke Kano, suka samu gawar wata Mata cikin wani gini da ba’a kammala ba da ake zargin ta fara zagwanyewa.
An dai gano gawar Matar ne lokacin da wasu magina ke kokarin fara aiki a kusa da kangon da gawar take sai sukaji wari ya dame su bayan sun leka kangon ne suka hangi gawar cikin mummunan yanayi.
Wani cikin maginan da ya bukaci a sakaye sunan sa ya bayyana cewa ‘lamarin ya tayar musu da hankali matuka sakamakon rashin iya gane fuskar matar, saboda rubewar da ta riga tayi’.
Wani magidan ci da suka taimaka wajen dauke gawar bayan zuwan dagaci da ƴan sanda ya bayyana cewar ‘zuwa yanzu ba’asan abunda ya yi sanadiyar mutuwar matar ba’.
Malam Inuwa Hassan, mazaunin yanki da lamarin ya faru ya shawarci mazauna unguwanni masu tasowa su Kara Sanya idanu tare da tabbatar da sun saka kofa matukar ginin su ya wuce tsayin mutum.
Freedom Radio ta Yi kokarin jin tabakin dagacin ƴankusa Alhaji Bala Isah, sai dai yaki cewa komai kan faruwar lamarin.
Rahoton: Abba Isa Muhammad
You must be logged in to post a comment Login