Jigawa
An yi garkuwa da malamin makaranta a jihar Jigawa
Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane sun sace wani malamin makaranta a karamar hukumar Auyo ta jihar.
Malamin mai suna Abdullahi Sani mai shekaru 35, ‘da ne ga wani dan siyasa a jihar, kuma malami ne a makarantar sakandare ta Birniwa a bangaren koyar da darasin Arabiyya.
Rahotanni sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun dira gidan na sa ne da ke unguar Shagari, inda nan take suka yi awon gaba da shi.
Ta cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Abdu Jinjiri ya fitar a jiya lahadi, ta bayyana cewa tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne da karfe biyu na daren jiya a wanda kuma tuni masu garkuwa da shi suka tafi da wayarsa.
You must be logged in to post a comment Login