Labarai
An yi wa ‘yan Nijeriya karin kudin lantarki
Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya ta amince da ƙara kuɗin wuta ga abokanan hulɗarsu da ke rukunin Band A da suke samun wuta tsawon sa’o’i 20 a rana.
Mataimakin shugaban hukumar, Musuliu Oseni ya bayyana hakan yayin taron manema labarai hukumar ta gudanar yau Laraba a Abuja.
Ya ce, a yanzu kwastamomin za su biya N225 kan kowane kilowatt sabanin a baya da suke biyan N66.
Musuliu Oseni ya kara da cewa, abokan hulɗarsu da ke samun wuta tsawon sa’a 20 a rana su ne kashi 15 cikin 100 na kwastamomin hukumar a Najeriya.
Ya kuma ce, hukumar ta kuma sauke kwastamomin da ke ajin Band A zuwa Band B masu samun wuta ƙasa da sa’o’i 20 a rana saboda rashin kamfanonin rarraba hasken lantarki na basu wutar da ta kamata.
Haka kuma, ya bayyana cewa ƙarin ba zai shafi kwastomomin da ke sauran tsarika.
You must be logged in to post a comment Login