Manyan Labarai
An zargi shugabar makaranta da amsar kudin dalibai
Wasu iyayen daliban makarantar sakandiren GGSS Sabon Gida da ke yankin Sharada a nan Kano, sun koka bisa yadda suka ce, mahukuntan makarantar sun bukaci ko wacce daliba kan ta bayar da 100 a kowacce jarrabawa guda 1 matsayin kudin jarrabawar Kwalafaiyn da za ta basu dammar tsallakawa zuwa aji 6.
A zantawar iyayen daliban da tashar Freedom Radio, sun bayyana cewa ‘ya’yan nasu sun shaida musu cewa shugaban makarantar ce ta umarce su da biyan kudin duk da cewa tun a baya gwamnatin jihar Kano ta sanar Da cewa karatu kyauta ne a fadin jihar.
Sai dai ko da Freedom Radio ta ziyarci makarantar domin jin ta bakin wadda ake korafin watau shugabar makarantar, ta musa zargin tana mai cewa ita ba ta san da maganar ba.
Kan haka ne Wakilin Freedom Radio Abba Ibrahim Lafazi ya dangana zuwa hukumar da ke kula da makarantun sakandire ta jihar Kano watau KSSSMB, inda ya samu ganawa da mai Magana da yawun hukumar Baba Ibrahim, wanda ya shaida masa cewa, binciken da suka yi ya gano cewa wani malami ne ke karbar kudin.
Haka kuma mai magana da yawun hukumar ta gidan malamai, ya kara da cewa, tuni hukumar ta umarci malamin kan ya dawo da kudin da ya karba daga hannun daliban.