Labarai
Ana cigaba da fuskatar kalubale a tawagar Kano ta PARA GAME
Tawagar jihar Kano na cigaba da fuskatar kalubale na kwam gaba kwam baya , tare da rashin kudin gudanar da aiyyukan gasar ya yinda aka shiga Rana ta karshe, da ake shirin kammala gasar.
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewar komai ya tsaya cik , sakamakon rashin kudin Inda ake kyautata zaton wasu daga cikin ‘yan wasan ka iya yin bore dangane da halin da suke ciki na rashin Tabbas.
A bangare daya tawagar da ta kunshi jami’an hukumar wasanni ta jihar Kano (KSSC) da masu lura da ‘yan wasan (Helpers) da masu horar wa suma suna cikin tsaka mai Wuya sakamakon rashin kudaden Alawus da hakan ta sa basa iya siyen Abincin da zasu ci.
Suma ‘yan Jaridun da suke tare da tawagar sun a cikin mawuyacin Hali da har kawo yanzu Babu wani da ga cikin jami’an hukumar wasanni ko gwamnatin jihar Kano da yayi musu karin haske kan makomar su, dangane da halin da suke ciki na rashin basu kudaden , wanda akayi musu alkwarin ba su da zarar tawagar ta sauka a birnin tarayya Abuja, ranar Litinin din da ta gabata.
Rahotannin Sirri da ‘yan Jaridun daga kafafen yada labarai da dama suka gudanar , ya Gano cewar an samu rarrabuwar kai da rashin tsara gudanar da aikin tawagar ta jihar a gasar , Wacce yanzu haka mafi akasarin ta ke kan hanyar dawowa jihar Kano cikin mummunan yanayi na tagayyara, in bada tsirarun ‘yan wasan da suka rage da zasu karasa wasan su na karshe , kafin su taho Kano.
Haka zalika ‘yan Jaridun sun yi bakin kokarin su don Jin ya akayi aka haihu a ragaya , daga bangaren Gwamnati sai dai hakan su ya kasa cimma Ruwa sakamakon ba wanda ya yarda ya yi magana akan lamarin.
A baya dai kafin tawagar ta taso zuwa wasan masu bukata ta musamman karo na biyu, na kasa a birnin tarayya Abuja, jami’an hukumar wasanni sun tabbatar dacewar gwamnatin jiha ya sahale kudaden da za a gudanar da tawagar wanda aka alkarwartawa dukkanin masu Ruwa da tsaki a tafiyar cewar za a Sallame su da zarar an sauka a Abuja, a Ranar Litinin din da ta gabata , sai dai kawo yanzu da Labarin nan ke fita Babu ko da Sisin Kobo da ya shigo dangane da Alkawarin na baya.
Rahoton: Aminu Halilu Tudun Wada
You must be logged in to post a comment Login