Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba mu da hannu a rikicin siyasar Rivers- Gwamnatin tarayya

Published

on

Ministan yaɗa labarai na Nijeriya, Idris Malagi ya ce, gwamnatin tarayya ba ta da hannu a rikicin siyasar da ake yi a jihar Rivers.

Ministan ya yi magana ne a gidan Talabijin na Channels yau Alhamis inda ya ce kasancewar wasu da ke cikin rikicin na cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu, hakan ba wai yana nufin gwamnatin APC ce ta kitsa halin da ake ciki ba a jihar.

“Ban gano wata shaida da zan iya cewa gwamnatin tarayya ce take ingiza rikici a jihar Rivers ba,” in ji ministan”.

Ya ƙara da cewa abu ne mai sauki a yaɗa jita-jita saboda wasu da ke cikin rikicin mutane ne da suke da kusanci da gwamnati”.

Malagi ya bayyana cewa akwai rikicin siyasa a wasu jihohin kamar Ondo kuma Shugaban ya sa baki aka warware rikicin da ya shafi ƴan jam’iyya daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!