Connect with us

Labarai

Ana fargabar mutuwar wani mutum sakamakon haɗarin mota a Kano

Published

on

Wata babbar motar dakon kaya ta kamfanin Ɗangote ta take baburin adaidaita sahu tare da bige motar gida.

Lamarin ya faru a mahaɗar kwanar kasuwa a titin sharaɗa da ke nan Kano.

Tuni dai jami’an tsaron ƴan sanda da jami’an kiyaye abkuwar haɗɗura da sauran su suka kai ɗaukin gaggawa tare da kwashe waɗanda abinda ya shafa don kai su asibiti.

Sai dai ana zargin guda daga cikin waɗanda haɗarin ya rutsa da su ya rasu nan ta ke, sakamakon danne shi da babbar motar ta yi.

Shaidaun gani da ido sun tabbatar da cewa lamarin ya faru da tsakar ranar Juma’a 01-10-2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!