Kiwon Lafiya
Ana kamuwa da cutar hanta ta hanyar cudanya da masu lalurar – Likita
Ana kamuwa da cutar hanta ta hanyar amfani da abubuwan yau da kullum da wanda yake dauke cutar yayi amfani da su.
Dr Rukayya Babale Shu’aibu ta sashen kula da lafiyar ciki a asibitin koyarwa na Aminu Kano ce ta bayyana hakan a wani bangare na bikin ranar tunawa da masu dauke da ciwon hanta ta duniya da ake gudanarwa a kowace ranar 28 ga watan Yuli.
Ta ce, ciwon hanta ya kasu zuwa rukuni-rukuni wadanda ke iya illata lafiyar mutum.
Ta kuma ce, ta hanyar yin gwaji ne kadai za a iya gane mai dauke da cutar.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ce ta ware duk ranar 28 ga watan Yulin kowacce Shekara, domin tunawa da masu fama da cutar ciwon hanta tare da lalubo hanyoyin magance ta a fadin duniya.
You must be logged in to post a comment Login