Labarai
Ana samun nasara a yaƙi da boko haram a Najeriya –Lai Muhammad

Gwamnatin tarayya ta ce Najeriya na samun nasara wajen yaƙar ayyukan ta’addanci.
Ministan yaɗa labarai da raya al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, yayin da yake hira a wani shirin BBC.
Ya ce, hujjar da za ta nuna cewa ana samun raguwar ayyukan ta’addanci a yanzu, shi ne yadda ƴan bindigar ke miƙa wuyan su tare da zubar da makaman su ga jami’an tsaron ƙasar nan a kwanakin nan.
Labarai masu alaƙa:
Rundunar soja ta samu nasarar lalata maboyar ‘yan ta’adda a Zamfara
Ministan ya musanta zargin da ake yi na cewa Najeriya ta gaza, inda ya alakanta hakan da irin rikicin da ake gani a Afganistan a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login