Jigawa
Ana zaman ɗar-ɗar a garin Yalwan Musari da ke Guri

Ana zaman dar-dar a garin Yalwan Musari dake karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa Biyo bayan rikicin da Ake zargin makiyaya da haifarwa kauyen.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaye sunan sa ya bayyanawa Freedom Radio yadda Lamarin faru tare da cewar har yanzu ana cikin fargaba.
Kan wannan batu ne ya sanya wakilinmu Abbah Isah Yakasai ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar Jigawa SP Lawal Shisu Adam in da ya bayyana cewa suna ci gaba da tattattara bayanai kan wannan batu.
You must be logged in to post a comment Login