Labarai
Ana zargi alkali da baiwa ‘yan sanda satar amsa
A kwanakin baya an samu labarin ‘yansanda da ake zargin sun daki wani matashi da dukan yayi sanadiyar rasa ransa, yayin da aka gurfanar da wadanda ‘yan sanda da ake zargi a gaban kotu.
Daya daga cikin shakikin marigayin ya koka da cewa Alkalin dake gabatar da shari’ar mai suna Mannir Madugu na fadawa daya daga cikin ‘yan sandan da suka daki marigayin irin tambayar da zai amsa, hakan yasa yayi wa alkalin magana akan meyasa zai ke baiwa ‘yan sandan satar amsa sai wannan alkali yace masa ya barshi aikin sa yake yi dalilin da yasa yayi shiru.
Walter Onnoghen:ya kalubalanci rashin cancantar alkalin kotun da’ar ma’aikata
Ya kara da cewa abunda ya bashi haushi da kuma takaici shine irin tambayar da wannan dan sanda yake masa na cewa wai shin marigayin yana da aljanu ne ko kuma wata cuta shi kuwa ya bashi amsa da cewa shi bai san wannan dan uwan na shi da wata cutar iska ko wani abu makamancin haka.