Labarai
Ana zargin hukumar KIRS da kara farshin lambar mota a kano
Rahotanni na nunar da cewa ana cigaba da samun zargi mai karfi akan hukumar tara kudaden shiga ta jihar Kano KIRS, dangane da karin kudin Lambar Mota.
A baya rahoton na nuni da cewa, farashin Lambar Motar baya wuce naira dubu 29,950, wanda ainihin kudin karfen lambar naira dubu 18,750 ne, ragowar kuma na takardu ne da kuma abinda yayi kama da haka.
Binciken da Freeom radio ta gudanar dai ya tabbatar da cewa ana siyarwa da lambar mota kan farashin naira dubu 8,250.
Rabiu Sale Rimin Gado shine mai Magana da yawun hukumar ta KIRS, ya musanta wannan zargi na karin kudin lambar.
Rabiu Sale Rimin Gado yace “ba a karawa lamba kudi ba sai dai lambobi da ke dauka hankali ko kumalamba ta musamman su ake karawa kudi”.
You must be logged in to post a comment Login