Labarai
Ana zargin kwamandan Hisbah da cin zarafi a Kano
Wata matashiya mazauniyar unguwar Tudun Maliki a nan Kano ta yi ƙorafin cewa kwamandan hukumar Hisbah na ƙaramar hukumar Kumbotso ya ci zarafinta.
Matashiyar wadda ta nemi a sakaye sunanta, ta shaidawa Freedom Radio cewa, mahaifiyarta ake bi bashi, har lamarin ya kai ga hukumar Hisbah ta jiha, inda a ka yi sulhu a kan mahaifiyar ta ta, za ta rika biyan dubu goma kowane wata.
Bayan wannan sulhu sai matashiyar ta fara biyawa mahaifiyarta bashin, sai kuma kwatsam kwamandan Hisbah na Kumbotso Gwani Murtala Mahmud ya aika jami’an Hisbah suka kamo ta tare da ɗan uwanta, aka kuma ƙulle ɗan uwanta har ya kwana a ofishin Hisbar inji matashiyar.
Ta kuma kara da cewa, kwamandan ya zageta, tare da yi mata kalamai na muzantawa.
Wakilin mu, Aminu Abdu Baka Noma ya tuntubi kwamandan Hisban na Kumbotso, Gwani Murtala Mahmud don jin ta bakinsa game da wannan zarge-zarge, sai dai ya ce, ba zai ce komai a kai ba, amma mu tuntubi kwamandan Hisbah na jiha, kuma wakilin namu ya tuntubi kwamandan Hisban na jiha Malam Muhammad Harun Ibn Sina wanda ya ce, sun samu rahoton kuma za su binciki gaskiyar lamarin.
Ku kasance da shirin Inda Ranka na yau da ƙarfe 9:30pm a Freedom Radio, don jin ƙarin bayani.
You must be logged in to post a comment Login