Labarai
Ana zargin makarantu masu zaman kan su da neman kudi
Duba da muhimmancin ilimi a fadin kasar nan aka samar da makarantu masu zaman kansu don cike gurbin gazzawar da makarantun gwamnati suka yi.
Sai dai abun ba haka yake ba a wannan lokaci kasancewar ana bude makarantun masu zaman kansu don neman kudi ga kuma rashin wadattun ajujuwa uwa uba kuma ga rashin bin ka’ida ba.
Tuni dai ake ta zargin cewa ana bude makarantun masu zaman kansu ne domin neman kudi.
Yawan bude makarantu marasa ajujuwa da yawa na nema zama ruwan dare a jihar nan, inda za a ga dakuna biyu ko daya ana mayar sa makarantun Nursery da firimare.
Al’ummar garin Kiru sun koka kan matsalar rashin asibitoci da makarantu
Za mu magance cunkoso a makarantu-KSSSMB
Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari
Amma dai masu bude irin wannan makarantun basa la’akari da fili ko gurin da yara zasu yi wasa.
Akwai unguwani da suke da irin wannan makarantu a kano wanda suka hada da Rijiyar Zaki da Kurna da dai sauran su.
Akan hakan ne wakiliyar mu Hafsat Abdullahi Danladi ta zanta da wasu iyaye kan ko suna la’akari da girman muhallin makarantun da Suke sa ‘ya’yan su, yayin da wasu ke cewa akasari sun duba saukin kudin makaranta.
Haka kuma wasu ke ganin cewar ba girman muhalli ba ne karatu illa dai ‘ya’yan su za su sami ilimin zamani
A nasa shugaban hukumar masu kula da makarantu masu zaman kansu ta Jihar Abba Dan kawu ya bayyana irin ka’idojin da ya kamata a bi wajen bude makarantu masu zaman kansu.
Ya ce an fi so a sami filin wasa mai girma da kuma wadatattun azuzuwa da dalibai za su dauki darusa a ciki.
Maitamakiyar shugaban kungiyar masu zaman kansu ta kasa Hajiya Maryam Magaji ta ce, kamata gwamnati ta rufe duk irin wannan makarantu da aka ma ta bude basi ka’ida ba musman masu budewa a daki guda koh biyu.
Masana a harkokin ilimi sun yi kira ga masu iri wanann dabi’ar da su gujii bude irin wadanan makarantun da ba bisa ka’ida ba.