Labarai
Ana zargin Miji da shanye jinin al’adar matar sa a Kano
Matar ta bayyana wa kotun cewar, maigidan nata yana yi mata surkulle har ta kai jallin yana ritsa ta da wuka akan lallai sai ta bashi dama ya shanye jinin al’adar ta domin ya biya bukatarsa.
Sai dai mijin matar da ake zargi da aikata wannan laifi yace kalan sharri ne kawai matar tasa tayi masa.
Daga bisani dai kotun ta sanya ranar ashirin da hutu ga watan gobe domin cigaba da sauraron shaidu .
Barrista Abdurrashid Balarabe Adam Dandago shine lauyan wadda ta shigar da kara ya kuma ya yi karin haske akan da’awar da suka yi a gaban Kotun a zamanta Kotun na yau.
Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya yi kokarin jin tabakin mijin matar amma abin ya faskara.
Sai dai maigidan nata ya yi kurin cewa, idan a aka zo kotun a ranar 24 ga watan gobe domin za mu ga abin mamaki a wannan rana.
You must be logged in to post a comment Login