Labarai
Ana zargin sarakunan mayun Kano na bogi ne
Masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewar ofishin karbar korafe-kaorafe da yaki da cin hanci da karbar rashawa na jihar Kano karkashin shugabancin Barrister Muhyi magaji Riming ado,ta kawo karshen karyace-karyace da wasu ke yi da sunan Maita.
Masu bibiyar shafukan jaridu da na Internet idan suna biye damu a ‘yan kwanakin nan an t- kai-ruwa-rana dagane da yadda wasu masu yan dabaru ke amfani da sunan maita ,har ma su dinga dora mutane a keken bera,karshe ma kaga an zo ana haddasa husuma a tsakanin mutane.
Rahotannin sun bayyana cewar, a kokarin dakile husumar ne ma yasa Anti corruption ta tashi haikan domin kawo karshen wnnan matsala, har ma aka kamo sarkin mayun Albasu da na Rege a karamar hukumar Wudil
Koda yake zuwan su hukumar sun ce ,kuskure aka samu domin dama can su ba mayu bane, kawai dai suna nutso da malafa ne domin samun abinci.
Wakilin mu Nasir Salisu Zango a wancan lokaci ya zanta da fadar sarkin mayun Kano dake Gano,wanda a tattaunawar tasu yake cewar sudai wadannan sarakuna sune dai suke karya amma shi fadar su sun gaji maita kuma suna aikata ta.
Alhaji Yahya Ali shine chiroman mayun Kano,na biyu mafi girman sarauta a fadar sarkin mayu dake garin Gano,ya hakikance akan cewar maitar tasu gaskiya ce.
Sarkin mayun boge ya karyata kansa
Mun kama Sarkin mayu na bogi-Muhiyi Magaji
Dole masu ruwa da tsaki su amince da hukuncin kotuna -Sarkin Kano
Sai dai a zantawar su dashi Nasiru Salisu Zango y ace tun da dai ana magan ne akan tantance gaskiya ya roke shi da ya kama shi alabasshi idan jiki sa ya gaya masa sai a sake shi kaga Kenan sai ya idar kuma idan juna nan sa surutu gaba ya idar ya kuma cigaba da girmama wannan fada ta sarkin mayun Kano,a cewar Zango
Amma kuma Zangon ya tabbatar da cewar Sarkin Mayun ya kasa kama shi kuma yaki aikata wani abu makamancin haka, wanda hakan ke nuni da cewar karya yake yi.
Har ila yau shima muyi magaji shugaban hukumar ta anti corruption ya bukaci chiroman na mayu wnada yake cewar yana kallon hanjin cikin mutane da ya gaya masa nau’in abin da yayi karin kumallo dashi ,nan ma dai aka yi tataburza.
Yanzu haka dai duka wadannan sarakunan mayu uku sun jadadda cewar dama can abin nasu ‘yan dabaru ne da nutso da malafa,sun kuma shaida cewar tun da sawun giwa ya taka na rakumi to sun zama sarakan tuwo da shayi maimakon sarakunan mayu.