Labarai
Anyi jana’izar Khaliphan Sheikh Ibrahim Inyass
A jiya Alhamis ne aka yi jana’izar fitaccen malamin nan Khalipha Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass wanda ya rasu a ranar Talata.
Marigayi Sheikh Khalipa Inyass shi ne na hudu a cikin jerin ‘ya’yan Sheikh Ibrahim Inyass, kuma shi ne Khalifansa na hudu cikin jerin khalifofinsa tun bayan rasuwar malamin a shekarar 1975.
Dubunnan al’ummar Musulmai ne daga sassa daban-daban na duniya suka halarci jana’izar marigayin a kasar Senegal, ciki har da tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II wanda yana daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a yayin jana’izar.
Sanusi II ya ce “Ina farawa da isar da ta’aziyyata, ga ‘yan uwa masu girma, bisa wannan babban rashi da muka yi, kamar yadda kuka sani, gamu anan al’umma da dama daga Najeriya sama da dubunnai, wasu daga Abuja, Kano da Legas da kuma sauran garuruwa, muna rokon Allah ya sada shehinmu da rahamarsa, ya kuma sanya shi a aljannah”.
Yanzu haka dai kasashe da dama da hukumomi ne ke ci gaba da aikewa kasar Senegal sakon ta’aziyya na rashin malamin.
A watan Yuni na shekara ta 2018 Sheikh Ahmed Inyas ya ziyarci fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da wasu manyan ‘yan Najeriya, ciki har da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u.
You must be logged in to post a comment Login