Labarai
Anyi yarjejeniyar sassauta farashi da masu sayar da Shinkafa a Kano
Hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta cimma yarjejeniya da kungiyar kamfanonin shinkafa domin sayar da babban buhu akan kudi naira dubu goma sha shida.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana haka bayan sun tattauna da shugabannin kamfanonin sarrafa shinkafa.
Muhuyi Magaji Rimin Gado ya kara da cewa shugabannin kamfanonin shinkafar sun bukaci da a bude wani gidan shinkafa da aka rufe a jihar Kano domin samun wadatacciyar ta.
Karin labarai:
Farashin shinkafa zai karye- Kamfanonin sarrafa shinkafa
Nan bada jimawa za’a fara fitar da shinkafa zuwa ketare -Nanono
A nasa bangaren Shugaban kungiyar kamfanonin masu shinkafa ta jihar Kano Abubakar Maifata ya ce zasu rika sayar wa da kasuwanni a naira dubu goma sha biyar ko naira dubu goma sha biyar da dari biyar inda su kuma za su sayar a naira dubu goma Sha shida.
Hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe korafe tace zata cigaba da tattaunawa da sauran masu sayar da kayayyakin bukata domin saukakawa al’umma a wannan lokaci na yaki da cutar Corona.
You must be logged in to post a comment Login