Labarai
APC ta lashe zabukan cike gurbi a Kano

APC ta lashe zaben ‘yan majalisar dokokin Ungoggo da KMC a jihar Kano
A mazabar Kano Municipal, dan takarar jam’iyyar APC Aliyu Nabil Daneji ya samu kuri’u 7,484, lamarin da ya ba shi nasarar lashe kujerar majalisar dokokin jihar Kano.
Hakazalika, a mazabar Ungogo, dan takarar APC Aminu Sa’ad Sa’ad ya samu kuri’u 8,975, inda ya lashe kujerar mazabar.
Sai dai bayanan da jaridar Daily Trust ta tattara sun ce manyan jam’iyyun adawa irinsu NNPP da ADC ba su shiga zaben ba da ya gudana a ranar Asabar.
You must be logged in to post a comment Login