Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta ‘kwace kujerar dan majalisar jiha daga hannun APC a Kano

Published

on

Kotun sauraron ‘korafin za’ben ‘dan majalisar dokokin jihar Kano, mai wakiltar ‘karamar hukumar Rogo ta ‘kwace kujerar ‘dan majalisar dokoki mai wakiltar ‘karamar hukumar Rogo daga hannun Magaji Dahiru Zarewa na jam’iyyar APC inda ta bai wa ‘dan jam’iyyar PDP Jibrin Isma’ila Falgore.
Da yake zantawa da manema labarai lauyan wanda ya shigar da ‘kara Jibrin Isma’ila Falgore da jam’iyyar APC, Barista Ibrahim Garba Waru, ya ce, kotun ta ce, ‘dan takarar jam’iyyar APC bai sauka daga kan mukaminsa ba lokacin da ya samu nasara a za’ben da ya gabata.
A cewar lauyan na PDP ‘dan takararta Jibrin Isma’il Falgore, Barista Ibrahim Garba Waru, alkalan kotun sun amince, cewa dukkannin ‘kuri’u da Alhaji Magaji Dahiru Zarewa na jam’iyyar APC ya samu haramtattu ne, saboda haka kotun ta ‘kwace nasarar da ya samu ta bai wa ‘dan takarar jam’iyyar PDP.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!