Labarai
Arewacin kasar nan bai taba neman ballewa ba -Bashir Tofa
Arewacin kasar nan bai taba neman ballewa ba -Bashir Tofa
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar NRC Alhaji Bashir Usman Tofa ya ce yankin Arewa bai taba neman ballewa daga Najeriya ba.
Alhaji Bashir Usman Tofa ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da gamayyar kungiyoyin daliban yankin Arewa wanda aka yi a harabar Jami’ar Bayero dake nan Kano.
Tsohon dan takarar ya ce yankin Aewacin kasar nan bai taba rajin a raba kasar nan ba ko kuma yunkurin ganin an kafa wata kasa bayan Najeriya ba.
A cewar sa yankin Arewacin kasar nan shi ne ginshinkin tallafawa kowanne yanki na kasar nan a don haka ba zai kawo wani cikas ba wajen ganin an sami rushewar kasar nan.
Ya shawarci ‘yan Arewacin kasar nan da su kara hakuri wajen samar da hadin kai baki daya.
Da yake jawabi tsohon shugaban ma’aikata ga shugaban majalisar datijjai na kasa Bukola Saraki Dr, Hakeem Baba Ahmad ya nuna bakin cikin sa kan yadda wasu daga cikin shugabanin masu rike da mukaman siyasa ke salon jagoranci a mukamai daban-daban da aka basu a kasar nan.
Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?