Labarai
Arsenal ta lashe kofin Kalubalen Ingila na-FA
Kungiyar kwallan kafa ta Arsenal, ta doke abokiyar hamayyar ta Chelsea daci biyu da daya, a wasan da aka fafata dazu a filin wasa na Wembly wanda hakan ya bata nasarar lashe kofin kalubale na FA.
Tun da fari dan wasan gaban Chelsea Christian Pulisic, ne ya saka kungiyar sa a gaba a minti na biyar da fara wasan, daga bisani dan wasan gaban Arsenal Pierre-
Emerick Aubameyang ya farkewa kungiyar tasa kwallan da Pulisic ya jefa ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 28.
Aubameyang, ya karawa Arsenal kwallan ta biyu a minti na 67, wacce ta tabbatar da nasar kungiyar akan Chelsea.
A yayin karawar Chelsea ta kammala wasan da ‘yan wasa goma, bayan da alkalin wasa ya bawa dan wasan tsakiyar ta Mateo Kovacic , Katin kora wato jan kati, sakamakon ketar da ya yiwa dan wasan Arsenal Xhaka.
Nasarar da Arsenal tayi, ya bata damar shiga cikin jerin Kungiyoyi uku da zasu wakilci Kasar Ingila a gasar kofin Europa a shekarar badi.
You must be logged in to post a comment Login