Labarai
Asalin dambarwar dake tsakanin Kwankwasiyya da Pantami
Asalin dambarwar dake tsakanin Kwankwasiyya da Pantami
Batun dambarwa tsakanin ministan sadarwa Dr, Isa Ali Pantami da kuma mabiya siyasar Kwankwasiyya ya samo asali ne tun bayan wa’azin da Dr, Isa Ali Pantami yayi a tafsirin Azumin Ramadana da ya gabata, yayin da ya caccaki jagoran darikar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Saurari jawabin da Dr, Isa Ali Pantami lokacin Tafsirin.
Sai dai wasu jama’a na kallon wannan wa’azi na Dakta Pantami a matsayin siyasa kasancewar tunda Sanata Kwankwaso yake jam’iyyar APC da Pantamin ke ciki, bai taba sukarsa akan wannan furuci da yake zargin Kwankwason yayi tun a lokacin yana gwamnan Kano wa’adi na biyu ba, a yayinda wasu kuma ke ganin cewar Dr, Isa Ali Pantami bai saurari cikakken jawabin Santan ba ma, hassali bambacin ra’ayin siyasa ne kawai.
Saurari cikakken jawabin na Rabiu Musa Kwankwaso
Martanin na Dakta Pantami dai ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, kasancewar ana tsaka da buga gangar siyasa a wancan lokacin, wannan batu dai ya sanya mabiya Kwankwasiyya da dama sambatu, har ta kai ana ganin cewa shine silar abinda suka rika acikin zuciyarsu har ta kai a haduwar da akayi a baya-bayan nan tsakanin Minista Pantami da kuma ‘yan kwankwasiyyar, a yayin da suke raka daliban da gidauniyar Kwankwasiyya ta tura karo karatu a kasashen waje, inda aka yi kacibis a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano dake nan Kano, inda wasu daga ‘yan kwankwasiyyar suka dinga yi masa ihu, wasu kuma na kokarin gaisawa dashi, dama bashi kariya kamar yadda bidiyoyin suka nuna.
Ra’ayoyin al’umma sun rabu gida biyu kan wannan batu inda wasu ke ganin ko kadan ba’a kyautawa ministan ba, kuma tamkar anci zarafinsa ne, inda Mallamai da dama dake bin akida iri daya da Mallam Pantami sukayi martani akai, ciki harda kungiyar Izala wadda shugaban kungiyar na kasa Mallam Abdullahi Balalau ya fito yayi alla wadai da faruwar al’amarin, haka ma dai an jiyo karin mallamai irin su Sheikh Lawal Abubakar Gadon Kaya suma sun mayar da martani mai zafi akai.
Sai dai wasu al’umma na ganin cewa mallaman dake jam’iyyar siyasa daya ne da mallam Pantami ke suka ga ‘yan kwankwasiyyar, kuma rashin adalci ne a zargi Kwankwaso kan wannan batu kasancewar baya wurin sanda lamarin ya faru, ba kuma shine ya bada umarnin aikata hakan ba.
A bangaren ‘yan kwankwasiyya kuwa na kallon hakan matsayin ramuwa ce irin ta siyasa domin kuwa wasu da dama na ikrarin hakan ya faru ne kasancewar yanzu Daktan na sanye da riga ne irin ta siyasa, izuwa yanzu dai har an samu wasu sun fito da tsofaffin bidiyo dake nuna ministan a shekarun baya yana maida zazzafan martana ga jam’iyyar adawa ta PDP.
Tuni dai rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta gayyaci jagororin darikar ta Kwankwasiyya kan faruwar wannan al’amari.
A siyasar Najeriya dai wannan ba sabon abu bane, domin kuwa tarihi na nuna cewa an sha jifa ko kuma yiwa manyan ‘yan siyasa a kasar irin wannan, idan dai baku manta ba ko kafin babban zaben shekarar 2019 da ya gabata, sai da wasu suka yiwa sanata Kwankwason irin wannan ihu yayinda yaje sallar jumu’a a garin Kaduna.
Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?